Tahiyya
اَلتَّحِيَّاتُ ِللهِ وَالصَّلَوَاتُ والطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُه .
Attahiyyatu lillahi wassalawatu wattayyibat, assalamu AAalayka ayyuhan-nabiyyu warahmatul-lahi wabarakatuh, assalamu 'alayna wa'ala ibadil-lahis-saliheen. Ash-hadu an la ilaha illal-lah, wa-ashhadu anna Muhammadan 'abduhu warasooluh.
Dukkan nau'in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.
Salati Ga Annabi, Tsira da Amincin Allah Su Tabbata A Gare shi, bayan Tahiya;
اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.
Allahumma salli 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala Muhammad, wa-'ala ali Muhammad, kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed.
Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda kayi salati ga Ibrahimu da alayen Ibrahim, lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da alayen Ibrahimu, lallai kai abon godewa ne, mai girma.
اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ. إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.
Allahumma salli AAala Muhammad wa-'ala azwajihi wathurriyyatihi kama sallayta 'ala ali Ibraheem, wabarik 'ala Muhammad, wa-'ala azwajihi wathurriyyatih, kama barakta 'ala ali Ibraheem. innaka Hameedun Majeed.
Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi salati ga alayen Ibrahim. Kuma ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma ga matansa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi albarka ga alayen Ibrahim. Lallai kai abin godewa ne, mai girma.
اَللّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ القَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ فِتْنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ.
Allahumma innee a'u'zu bika min 'athabil-kabr, wamin 'azabi jahannam, wamin fitnatil-mahya walmamat, wamin shari fitnatil-maseehid-dajjal.
Ya Allah ina neman tsari da Kai daga azabar kabari, da azabar Jahannama, da fitinar rayuwa da ta mutuwa, da sharrin fitinar Dujal shafaffe.
اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ مِـنْ عَذابِ القَـبْرِ، وَأَعـوذُ بِكَ مِـنْ فِتْـنَةِ المَسيحِ الدَّجّـالِ، وَأَعـوذُ بِكَ مِـنْ فِتْـنَةِ المَحْـيا وَالْمَمَـاتِ. اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ مِنَ المَأْثَـمِ وَالمَغْـرَم .
Allahumma innee a'u'zu bika min azabil-kabr, wa-a'u'zu bika min fitnatil-maseehid-dajjal, wa-a'u'zu bika min fitnatil-mahya walmamat. Allahumma innee a'u'zu bika minal-ma'thami walmaghram.
Ya Allah! Ina neman tsarinka daga azabar kabari, kuma ina neman tsarinka daga fitinar Dujal shafaffe, kuma ina neman tsarinKa daga fitinar rayuwa da ta mutuwa. Ya Allah ina neman tsarinka daga laifi da bashi.
اَللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْمًا كَثِيراً وَلاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ، فَاغْفِرْلِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ وَارْحَمْنِي، إِنَّكَ أَنْتَ الغَفُورُ الرَّحِيم .
Allahumma innee zalamtu nafsee zulman katheeran wala yaghfiruz-zunooba illa ant, faghfir lee maghfiratan min 'indika warhamnee, innaka antal-Ghafoorur-Raheem.
Ya Allah! Hakika ni na zalunci kai na, zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai Kai. Saboda haka Ka gafarta mini, gafara daga gare Ka, kuma Ka ji kai na, lallai Kai ne mai yawan gafara, mai yawan jin kai.
اَللَّهُمَّ اغْفِرْلِي مَاقَدَّمْتُ وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، وَمَا أَسْرَفْتُ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي. أَنْتَ الْمُقَدِّمُ، وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.
Allahummagh-fir lee ma kaddamtu, wama akhkhart, wama asrartu wama a'alant, wama asraftt, wama anta a'alamu bihi minnee, antal-mukaddimu wa-antal-mu-akhkhiru la ilaha illa anta.
Ya Allah ka gafarta mini abin da ya wuce da abin da zai zo, da abin da na boye da abin da na bayyana, da kuma abin da Kai ne Ka fi fi ni saninsa. Kai ne Mai gabatarwa, kuma Kai ne Mai jinkirtawa; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.
اَللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِك، وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ.
Allahumma a'innee 'al
No comments:
Post a Comment