Friday, 7 July 2017

ADDU'AR RUKU'U DA DAGOWA DAGA RUKU'U


Addu'ar Ruku'u

سُبْـحانَ رَبِّـيَ الْعَظـيم . (ثلاثَ مَرَّاتٍ)
 Subhana rabbiyal-a'zeem (3)

Tsarki ya tabbata ga Ubangijin mai girma (Sau uku).


سُبْحانَكَ اللّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِك، َاللَّّهُمَّ اغْفِرْ لِي.
Subhanakal-lahumma rabbana wabihamdik, allahummagh-fir lee

Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu, tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.


سُبُّوحٌ قُـدُّوسٌ، رَبُّ الْمَلاَئِكَةِ وَالرُّوحُ .
Subboohun kuddoos, rabbul-mala-ikati warrooh.

(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala'iku da Jibrilu.


اَللَّهُمَّ لَكَ رَكَعْتُ وَبِكَ آمَنْتُ، ولَكَ أَسْلَـمْتُ، خَشَعَ لَكَ سَمْعِي، وَبَصَرِي، وَمُخِّي، وَعَظْمِي، وَعَصَبِي، وَمَا اسْتَقَـلَّ بِهِ قَدَمِي.
Allahumma laka raka'atu, wabika amantu, walaka aslamtu, khasha'a laka sam'ee, wabasaree, wamukhkhee, wa'azmee, wa'asabee, wamas-takalla bihi kadamee.

Ya Allah! Gare ka na yi ruku'u, kuma da Kai na yi imani, kuma gare ka na mika wuya. Jina ya yi kaskanci gare Ka, haka ma ganina da bargona, da kashina, da jijiyata, da kuma abin da kafata ke dauke da shi.
سُبْـحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، والمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءُ، وَالْعَظَـمَة.
Subhana thil-jabaroot, walmalakoot, walkibriya, wal'azamah.

Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka, da girma.




Addu'ar Dagowa daga Ruku'u

سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ.
Sami'al-lahu liman hamidah

Allah Ya ji wanda ya gode masa.


رَبَّنـا وَلَكَ الحَمْـدُ حَمْداً كَثِيراً طَيِّـباً مُـبَارَكاً فِيهِ .
Rabbana walakal-hamdu hamdan katheeran tayyiban mubarakan feeh.

Ya Ubangijinmu! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sawa albarka a cikinsa.


مِلْءَ السَّمَوَاتِ وَمِلْءَ الأَرْضِ، وَمَا بَيْنَهُمَا، وَمِلْءَ مَا شِئْتَ مِنْ شَيءٍ بَعْدُ. أَهْلَ الثَّنَاءِ وَالْمَجْدِ، أََحَقُّ مَا قَالَ العَبْدُ، وَكُلُّنَا لَكَ عَبْدُ. اَللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَـيْتُ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ. 
Mil-as-samawati wamil-al-ard, wama baynahuma, wamil'a ma shi'ta min shay-in ba'd, ahlath-thana-i walmajd, ahakku ma kalal-'abd, wakulluna laka 'abd. Allahumma la mani'a lima a'tayta, wala mu'tiya lima mana'ta, wala yanfa'u zal-jaddi minkal-jaddu.

Ya Ubangiji! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, (yabo) mai Cika sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, mai cika duk wani abu da Ka so bayan haka. Ya wanda ya cancanci yabo da daukaka. (wannan yabo) shi ne mafi cancantar abin da bawa ya fada, kuma dukkanninmu bayi ne gare Ka. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar, kuma babu mai byar da abin da Ka hana, kuma wadata ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.


No comments:

Post a Comment