Addu’a yayin kiran Sallah :
Wanda ya ji kiran sallah zai fadi dukkan abin da ladanin yake fadi, sai dai idan yace;
حَيَّ عَلَى الصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى الْفَلاَحِ.
Hayya Alas Salah, Hayya Alal Falah.
Ku taho ga Sallah, ku taho ga babban rabo.
Maimakon haka sai shi ya ce:
لا حَـوْلَ وَلا قُـوَّةَ إِلاّ بِالله.
La hawla wala kuwwata illa billah.
Babu daraba, babu karfi sai da Allah.
وَأَنا أَشْـهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـريكَ لَـهُ، وَأَنَّ محَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسُـولُهُ ، رَضِيـتُ بِاللهِ رَبَّاً ، وَبِمُحَمَّـدٍ رَسُـولاً وَبِالإِسْلامِ دِينًا .
Wa-ana ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-anna Muhammadan AAabduhu warasooluh, radeetu billahi rabban wabimuhammadin rasoolan wabil-islami deena.
Ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Kuma Allah shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shi ne Manzo, kuma Musulunci shi ne addini.
Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sannan ya ce:
اللّهُـمَّ رَبَّ هَذِهِ الدّعْـوَةِ التّـامَّةِ وَالصّلاةِ القَـائِمَة آتِ محَـمَّداً الوَسيـلةَ وَالْفَضـيلَة وَابْعَـثْهُ مَقـامًـا مَحْـمُوداً الَّذِي وَعَـدْتَهُ إِنَّـكَ لا تُـخْلِفُ الْمِيـعَادَ.
Allahumma rabba hathihid-da'watit-tammah, wassalatil-ka-imah ati Muhammadan alwaseelata wal-fadeelah, waba'ath-hu makaman mahmoodan allazee wa'adtahu, innaka la tukhliful-mee'ad.
Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe mu a matsayi abin godewa, wannan wanda Ka yi masa alkawarinsa. Lallai kai ba ka saba alkawari.
Sannan ya yiwa kansa addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu'a a wannan lokaci ba a kin karbarta.
Addu'ar Bude Sallah (watau Bayan An yi Kabbarar Harama)
اَللَّهُـمَّ باعِـدْ بَيـنِي وَبَيْنَ خَطـايايَ كَما باعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبْ ، اَللَّهُـمَّ نَقِّنِـي مِنْ خَطايايَ كَمـا يُـنَقَّى الثَّـوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسْ ، اَللَّهُـمَّ اغْسِلْنِـي مِنْ خَطَايَـايَ بِالثَّلـجِ وَالمـاءِ وَالْبَرَدْ .
Allahumma ba'id baynee wabayna khatayaya kama ba'adta baynal-mashriki walmaghrib, allahumma nakkinee min khatayaya kama yunakkath-thawbul-abyadu minad-danas, allahummagh-silnee min khatayaya biththalji walma'i walbarad.
Ya Allah! Ka nisanta tsakanina da laifuffukana kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma; Ya Allah! Ka tsarkake ni daga laifuffukana kamar yadda ake tsarkake farar tufa daga dauda, Ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffukana da kankara da ruwa da raba.
سُبْـحانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْـدِكَ وَتَبارَكَ اسْمُـكَ وَتَعَـالَى جَـدُّكَ وَلا إِلهَ غَيْرُكَ.
Subhanakal-lahumma wabihamdika watabarakas-muka wata'ala jadduka wala ilaha ghayruk.
Tsarki ya tabbata gareKa, Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun sunanka sun yawaita; mulkinka da girmanka sun daukaka; babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.
وَجَّهـْتُ وَجْهِـيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمـَوَاتِ وَالأَرْضَ حَنِـيفَاً وَمَـا أَنَا مِنَ المشْرِكِينَ، إِنَّ صَلاَتِـي، وَنُسُكِي، وَمَحْـيَايَ ، وَمَمَاتِـي ِللهِ رَبِّ العالَمِينَ، لاَ شَرِيـكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِـمِينَ. اَللَّهُـمَّ أَنْتَ المَلِكُ لاَ إِلهَ إِلاَّ أَنْتَ ،أَنْتَ رَبِّـي وَأَنَـا عَبْـدُكَ ، ظَلَمْـتُ نَفْسِـي وَاعْـتَرَفْتُ بِذَنْبِـي فَاغْفِرْ لِي ذُنُوبِي جَمِيعاً إِنَّـهُ لاَ يَغْـفِرُ الذُّنـُوبَ إلاّ أَنْتَ .وَاهْدِنـِي لأَحْسَنِ الأَخْلاقِ لاَ يَهْـدِي لأَحْسَـنِهَا إِلاَّ أَنْـتَ، وَاصْـرِفْ عَـنِّي سَيِّئَهَـا، لاَ يَصْرِفُ عَـنِْي سَيِّئَهَـا إِلاَّ أَنْـتَ، لَبَّـيْكَ وَسَعْـدَيْكَ، وَالْخَـيْرُ كُلُّـهُ بِيَـدَيْـكَ، وَالشَّرُّ لَيْـسَ إِلَـيْكَ، أَنَا بِكَ وَإِلَيْـكَ، تَبَـارَكْتَ وَتَعَـالَيتَ أَسْتَغْـفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ.
Wajjahtu wajhiya lillazee fataras-samawati wal-arda haneefan wama ana minal-mushrikeen, inna salatee wanusukee wamahyaya wamamatee lillahi rabbil-'alameen, la shareeka lahu wabithalika umirtu wa-ana minal-muslimeen. Allahumma antal-maliku la ilaha illa ant. anta rabbee wa-ana 'abduk, zalamtu nafsee wa'taraftu bizanbee faghfir lee thunoobee jamee'an innahu la yaghfiruz-zunooba illa ant.wahdinee li-ahsanil-akhlaki la yahdee li-ahsaniha illa ant, wasrif 'annee sayyi-aha la yasrifu 'annee sayyi-aha illa ant, labbayka wasa'dayk,walkhayru kulluhu biyadayk, washsharru laysa ilayk, ana bika wa-ilayk, tabarakta wata'alayt, astaghfiruka wa-atoobu ilayka.
Na juya fuskata ga wanda ya kagi halittar sammai da kassai, ina mai karkata ga addini na gaskiya, kuma ni ba na cikin mushrikai. Lallai sallata da ayyukan ibadata da rayuwata da mutuwata na Allah ne, Ubangijin talikai; babu abokin tarayya a gare Shi, kuma da wannan aka umarce ni, kuma ni ina daga Cikin Musulmi. Ya Allah! Kai ne Sarki, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai; kai ne Ubangijina, kuma ni bawanka ne, na zalunci kaina, kuma na tabbata da zunubina; Ka gafarta mini zunubaina dukkanninsu, ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai; Ka gusar da miyagunsu daga gare ni, babu wanda zai gusar da miyagunsu daga gareni sai Kai. Amsa maka, da biyayya gare ka bayan biyayya; kuma arziki naka ne, kuma alherin dukkaninsa yana hannunka, sharri kuma ba a danganta shi gare Ka. Ni kuma dacewata tana gare Ka, kuma gare Ka nake fakewa. Alherinka ya yawaita, kuma Ka daukaka. Ina neman gafarrka, kuma ina tuba gare Ka.
اللّهُـمَّ رَبَّ جِـبْرَائِيلَ، وَمِيكَـائِيلَ، وَإِسْـرَافِيلَ، فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ، عَالِمَ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ أَنْتَ تَحْكُمُ بَيْـنَ عِبَادِكَ فِيمَا كَانُوا فيهِ يَخْتَلِفُونَ. اهْدِنِي لِمَا اخْتُلِفَ فِيهِ مِنَ الْحَقِّ بِإِذْنِكَ، إِنَّـكَ تَهْـدِي مَنْ تَشَـاءُ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقَيمٍ.
Allahumma rabba jibra-eel, wameeka-eel, wa-israfeel fatiras-samawati walard, 'alimal-ghaybi washshahadah, anta tahkumu bayna 'ibadika feema kanoo feehi yakhtal
Please to your brothers and sisters
No comments:
Post a Comment